Jiya Asabar dubban farar hula cike da murna sun dawo birnin Manbij na arewacin Siriya da aka masa kaca-kace, kwana guda bayan da mayakan da ke samun goyon bayan AMurka su ka fatattaki mayakan kungiyar ISIS mai tsattsauran ra'ayi, daga wannan tunga tasu da ke daura da iyakar Turkiyya.
Hotunan bidiyo a gidan talabijin na Kurdistan 24, na nuna yadda wasu motoci ke ta fama a titunan da ke cike da baraguzai. Sannan sai ga dinbin jama'a, mata da maza da yara , su na dawowa da kafa daga wasu sassan bayan gari, inda su ka fake yayin da mayakan Jaddada Dimoradiyya a Siriya (SDF) ke yakin kubutar da wannan garin, wanda ada aka san shi da zaman lafiya.
Maza na ta aske gemu cikin murmushi sannan mata na ta kona bakakaken nikabi, su na ta nuna bijirewa ga irin dokokin da kungiyar ISIS ta kakaba lokacin da ta ke iko da yankin.
Mai magana da yawun wasu sojojin yankin masu alaka da SDF ya gaya ma kafar labarai ta Reuters cewa, "Yau ne rana ta farko da rayuwa ke dawowa kamar yadda ta ke ada."
Masu tsattsauran ra'ayin sun arce daga birnin ranar Jumma'a , su ka danna zuwa garin kan iyaka na Jarabulus, wanda ke karkashin ikon ISIS, tare da wasu farar hula masu yawan kusan dubu biyu.