Shahararren dan wasan ninkayan nan na Amurka, Michael Phelps, ya ci babbar lambar yabo ta zinari a karo na 23 na shigarsa wasan 'Olympic;' wanda kuma shi ne karo na biyar da ya ci a gasar da ake yi a Rio, gasar da ka iya zama ta karshe da zai yi a 'Olympic' a rayuwarsa.
Michael Phelps, wanda shi ne ya fi cin lambobin yabo a tarihin 'Olumpic,' ya zabura ya wuce dan Burtaniya, ya samar wa Amurka nasara.
Zagayen farko na gasar, wanda iyo da baya ne, ya zama wata dama ta kafa tarihi ga Ryan Murphy na Amurka, hasalima wannan ya karfafa gwiwar daukacin 'yan wasan AMurka, ta yadda sauran lokacin da ya rage na gasar ya zama tamkar lokacin kafa tarihi garesu.
Haka zalika, 'yan wasan ninkayar mata na Amurka, sun ci zinari a gasar iyon mita 100 da ake yi sau 4.
Sannan a ranar ta karshe ta gasar iyo a Rio, Gregorio Paltrinieri na Italiya, ya ci zinari a tsaren iyo mai ban wahala na maza - na mita 1,500 na freestyle. Shi kuma Connor Jaeger na Amurka ya ci azurfa.
Tunda farko, Pernile Blume na Denmark ya zarce Simone Manuel na Amurka, ya ci gasar freestyle ta mita 50.