Zan Shiga Makaranta Domin Shiga Aikin Soja In Taimakawa Kasa Ta

fata na in yi karayu in shiga soja domin taimakawa kasata, Agusta 05, 2015

A yayin da yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ke fama da hare haren 'yan ta'adda wanda ya yi sanadiyyar rayukan jama'a da dama da kuma tilasta wa wasu da dama barin muhallan su, Aliyu Shu'aibu matashi ne dan shekara goma sha tara wanda ya ce yana mai matukar kishin kasar sa.

A tattaunawar su da wakiliyar dandalin VOA Baraka Bashir, Matashin ya bayyana ra'ayin sa ne musamman ta yadda yake bada kokari wajan koyon sana'ar sa ta hannu wato gyaran mashin, da kuma irin burin sa na komawa makaranta domin samun damar shiga aikin soja.

Ya kara da cewa "babban buri na shine in gama koyon aikin da nake yi, in koma makaranta, sannan in daura dammara wato in shiga aikin soja domin ina maukar so in taimakawa kasata yaki da masu tada kayar baya, in kuma taimakawa na baya da ni"

Daga kar she matashin ya nuna rashin jin dadin sa musamman yadda matasa da dama ke zaman kashe wando mai makon koyon sana'a kamar yadda ya ke yi da kuma rashin kishin kasar su.

Ga rahoton Baraka Bashir.