Jam’iyyar PDP ta soki daftarin kasafin kudin 2025 da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar, inda ta bayyana shi da wanda ba za’a iya aiwatarwa ba kuma “mai yawan rufa-rufa da rashin gaskiya a cikinsa.”
A sanarwar daya fitar a jiya Laraba, sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunaba, yace babu lissafin talaka a cikin kasafin, inda ya yi gargadin cewa aiwatar da shi zai kara tabarbara matsalolin tsaro da fatara da halin rashin tabbas a fadin Najeriya.
Tinubu ya gabatar da daftarin kasafin kudin 2025 na Naira tiriliyan 49.7 a gaban zaman hadin gwiwar majalisun tarayya, inda ya warewa fannonin tsaro naira tiriliyan 4.91 sai ayyukan raya kasa da zasu ci naira tiriliyan 4.06 da fannin kiwon lafiya da aka warewa naira tiriliyan 2.48 sai kuma ilimi da zai ci naira tiriliyan 3.52.
Sai dai jam’iyyar adawar ta soki gabatar da kasafin kudin, inda tayi zargin cewa an cika shi da alkaluman tattalin arzikin da ba’a tantance ba da alkawuran yakin neman zaben da babu komai a ciki.
PDP ta soki gwamnatin tinubu da gaza zuba jarin azo a gani a muhimman fannoni irinsu aikin gona da lantarki da man fetur da kuma kanana da matsakaitan masana’antu.