An yi asarar rayuka da dama a turmutsutsin da ya faru yayin wani bikin kalankuwa a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Kakakin ‘yan sadan jihar Oyo SP Osefiso ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da aka rarrabawa manema labarai a Ibadan.
SP Osifeso ya tabbatar da mutuwar kananan yara maza da mata 35 a turmutsutsi da suka je makarantar Islamiyya da ke shiyar Bashorun a Ibadan don karbar kyaututtukan kirsimeti daga tsohuwar mai ɗakin Sarki Ooni na Ife, Naomi Silekunola Ogunwusi da mai gidan rediyon Agidigbo FM, Oriyomi Hamzat waɗanda su ne ake yi wa kallon haddasa al'amarin.
Duk da cewa ba’a kai ga tantance adadin mutanen da al’amarin ya shafa ba, wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna yaran da turmutsutsin ya rutsa dasu a shiyar Bashorun na birnin Ibadan a jiya laraba.
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana lamarin da ranar takaici ga gwamnatin jihar Oyo sannan ya jajantawa iyayen da suka rasa ‘ya’yansu.
A cewar Makinde, hukumomin tsaro sun kama wadanda suka shirya kalankuwar kuma jihar za ta tabbatar sun fuskanci shari’a.
A saurari rahoton Hassan Tambuwal:
Dandalin Mu Tattauna