Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fannoni Da Ke Kan Gaba A Kasafin Kudin 2025 Da Shugaba Tinubu Ya Gabatar


Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Tinubu ya bayyana aniyarsa ta sabunta tattalin arziki, inda ya godewa ‘yan Najeriya game da jurewar da suka nuna a tafiyar gwamnatinsa ta kawo sauyi a watanni 18 din da suka shafe tare.

Tsaro, raya kasa, lafiya da ilimi ne fannonin da suka samu kaso mafi tsoka a kasafin kudin Naira tiriliyan 47.9 da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatarwa zaman hadin giwar zaurukan majalisun kasar 2 da maraicen yau Laraba.

“Ina mai farin cikin gabatar wa wannan zaman hadin gwiwar majalisun tarayya mai alfarma da kasafin kudin 2025 mai taken: “kasafin sake farfado da tsaro da wanzar da zaman lafiya da yalwar arziki,” a cewar Tinubu yayin da yake kammala jawabinsa.

Tun da fari a jawabin nasa, shugaban kasar ya zayyano fannonin da kasafin ya baiwa fifiko kamar haka; tsaro zai samu Naira tirilyan 4.91, raya kasa da zai samu Naira tiriliyan 4.06, lafiya mai naira tiriliyan 2.4 da kuma ilimi da zai samu Naira tiriliyan 3.5.

“Kasafin kudin ya yi hasashen samun raguwar hauhawar farashin kaya daga kaso 34.6 da yake a halin yanzu kaso 15 cikin 100 a shekara mai kamawa (2025) yayin da shima canjin dala zai inganta daga Naira 1, 700 zuwa 1, 500.”

Ya bayyana aniyarsa ta sabunta tattalin arziki, inda ya godewa ‘yan Najeriya game da jurewar da suka nuna a tafiyar gwamnatinsa ta kawo sauyi a watanni 18 din da suka shafe tare.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG