Kasafin kudin da aka ba taken, "tabbatar da zaman lafiya da bunkasa wadata", shi ne kasafin kudi na biyu da Shugaba Tinubu ya gabatar gaban Majalisa tun da ya hau karagar mulkin kasar a ranan 29 ga watan Mayu na shekara 2023.
A wannan kasafin ya ware wa tsaro kudi mafi tsoka da ya kai Naira triliyan 4.91, sannan ya ba bangaren kiwon lafiya Naira triliyan 2.48, wanda ya zama na 4 mafi girma bangaren ilimi ya samu Naira triliyan 3,52, Naira triliyan 4.6 kuma na ababen more rayuwa.
Shugaba Tinubu ya kara bayana Kudurin gwamnati na samar da tsare-tsare na kula da lafiya ta duniya da nufin karfafa tsarin kiwon lafiya a matakin farko a fadin kasar. Tinubu ya ce gwamnatin sa za ta tallafa wa manoma tare da samar da kudaden da za su inganta noma.
Dan Majalisar Wakilai daga Jihar Kano kuma Shugaban Kwamitin Kula da Kasafin Kudi, Kabir Abubakar Bichi ya yi tsokacin kan abinda zai biyo baya a batun kasafin kudin inda ya ce Majalisa za ta fara aiki akan kasafin ba tare da bata lokaci ba, kuma za a gayyato wadanda abin ya shafa daga Ministoci da shugabanin hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki, har sai an kawo rahoto a gaban Majalisa ta amince kafin a kaiwa Shugaban Kasa ya sa hannu.
A nasa bayanin, Sanata Mai Wakiltan Nasarawa ta Yamma Ahmed Aliyu wannan kasafin da ya fi kowanne girma, alamu ne na canji, sai dai za a ji daga bakin 'yan kasa ko sun gamsu da kasafin kafin Majalisa ta amince da shi. Ya ce, idan haka ta faru to za a ce an samu nasarar aiki akan kasafin sai Shugaba ya yi abinda ya kamata. Wadada ya ce aiki ne da Majalisa za ta dukufa akai ka'in da na'in.
Sai dai wasu 'yan adawa na ganin babu wani abu da 'yan kasa za su amfana a wannan kasafin, ganin cewa ana aiwatar da kasafin kudin shekarar 2023 ne kuma har yanzu ba a gama ba.
Dan Majalisar Wakilai daga Karamar Hukumar Katagum ta jihar Bauchi Auwalu Abdu Gwalabe ya ce akwai abin dubawa a wannan kasafin da ma sauran wadanda ba a gama aiwatar da su ba. Bisa ga cewarsa, su 'yan adawa suna ganin batun cewa, za a gayara abubuwa kama daga tsaro, da hanyoyin sufuri, da harkar noma, duk zance ne kawai na kanzon kurege. Gwalabe ya ce babu wani tasiri da za gani a wannan kasafin saboda a yanzu ana aiwatar da kasafi da ba'a gama da shi ba, saboda haka labarin kanzon kurege ne kawai.
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya tabbatar wa kasa cewa, Kasafin kudin bana da ba a fara aiwatar da shi ba, za a cigaba da aiwatar da shi har watan Yuni na shekara mai zuwa.
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna