Majalisar Dokokin Najeriya ta tsawaita wa’adin aiwatar da kasafin kudin 2024 da watanni 6, kamar yadda Shugaban Majalisar Dattawan kasar Godswill Akpabio ya bayyana a yau Laraba yayin gabatar da kasafin kudin 2025 da shugaba Bola Tinubu ya yi.
“Mun ga irin kwazon da aka nuna wajen aiwatar da kasafin 2024.
“Duba da wannan gagarumar nasara, mun dacewar mu tsawaita wa’adin aiwatar da kasafin kudin 2024 zuwa ranar 30 ga watan Yunin, 2025.
“Nan gaba kadan za’a gabatar muku da dokar data bada damar tsawaita wa’adin domin ku amince” a cewar akpabio.
Adadin kasafin kudin Tinubu na 2025 na Naira tiriliyan 47.9 ya dara na 2024 da Naira tiriliyan 20.
A watan Disamban 2023, Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2024 na naira Tiriliyan 27.5, wanda ya kasance kasafinsa na farko ga Majalisar Dokokin Najeriya.
A wannan watan kuma, Majalisar Dattawa ta kara yawan kasafin da Naira tiriliyan 1.2 tare da amincewa da Naira Tiriliyan 28.7 a matsayin kasafin kudin 2024.
Dandalin Mu Tattauna