Shugabannin sun yi kiran ne jim kadan da kammala taronsu na wata-wata a birnin Abeokuta fadar gwamnatin jihar Ogun jiya Lahadi.
Alhaji Ibrahim Bodinga, ya kira Hausawa su yiwa Allah kada su tafi koina yana mai kiran kowa ya zauna lafiya.
Da wakilin Muryar Amurka ya tambayeshi dalilin da ya sa sai yanzu suka yi kiran sai ya ce yanzu suka ga mutanensu na sulalewa zuwa arewa.
Ya ce idan an je tashar motocin dake zuwa arewa duk hausawa ne gaba daya ke barin yankin.
Dangane da ko suna tsoron sake aukuwar irin tashin hankalin da ya biyo bayan zaben 2011, sai Alhaji Bodinga ya ce su basu taba ganin irin wannan tashin hankalin ba a yankinsu.
Shi ma Isa Sokoto jami'in hulda da jama'a na shugabannin ya ce idan dan arewa zai tafi ya jefa kuri'a a arewa to babu laifi ya yi hakan.
Amma wanda ya yi rajista a kudu ya tsaya ya kada kuri'arsa a kudu sannan shugabannin sun ce idan mutum ya yi rajista a arewa koda bashi da kudin zuwa arewan kungiyar za ta yi masa ciko ya tafi.
Alhaji Usman Danbaba shugaban masu sayar da albasa ya kira jama'ar hausawa na jihar Ogun da su kwantar da hankalinsu.
Hakan dai na faruwa ne yayin da babban zabe ke ci gaba da karatowa a Najeriya inda Shugaba Goodluck Jonathan zai fuskanci dan takarar jam'iyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari.
Wasu yankunan Najeriyar sun fuskanci tashe-tashen hankula a zabukana da aka yi a baya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dukiyoyi da dama.
Ga karin bayani a rahoton Hassan Umaru Tambuwal.
Your browser doesn’t support HTML5