Wannan hasken da aka samu ya biyo bayan jawaban da bangarorin biyu suka yi bayan ganawarsu da shugaban hukumar zabe Farfasa Attahiru Jega.
Shugaban hukumar zabe ya bayyana masu irin shirye-shiryen da hukumarsa tayi kana su sojojin suka bayyana irin nasarorin da suka samu a yaki da Boko Haram da kuma shirin tabbatar da tsaro a lokacin zabukan.
Manyan sojojin sun gamsu cewa shirye-shirye sun yi nisa kuma za'a gudanar da zaben kamar yadda aka tsara. Farfasa Jega yace shi abun da ya fahimta a taron shi ne kowa ya ga shirin da aka yi kuma yakamata a yi zabukan da inganci cikin kwanciyar hankali. A tabbatar da tsaro wanda zai dakile duk wani shirin tashin tashinar hankali ko wani shirin magudi na zabe.
Jega yace a fahimtarsa sojoji ashirye suke su bada duk wani taimako da zai tabbatar da samun cikakken tsaro. Yace tun shekarar 2011 bayan an gama zabuka INEC tayi tanade-tanade na tabbatar da gudanar da zabukan wannan shekarar cikin lafiya amma shirinsu ya jibanci abun da dokar kasa ta tsara. Misali dokar kasa tace za'a iya kiran sojoji idan ta baci domin su taimakawa 'yansanda a kwantar da kowace tarzoma ta taso.
Farfasa Jega yace bai ga wata alama ba cewa sojoji na iya fitowa su ce kada a yi zabe a ranakun da aka tsayar. Babu wata alama akwai shiri a koina cewa ana yunkurin sake dage zaben. Yace su a fahimtarsu a INEC babu ma wani lokaci bisa ga doka da za'a iya sake dage zabe. Bisa ga tsarin mulki dole ne a yi zaben kafin 29 ga watan Afirilu. Idan aka sake dage zaben za'a sabawa kundun tsarin mulki. Yace babu wani dalili ko alama da zasu sa a sake dage zaben.
Ga rahoton Umar Faruk Musa..