Barrister Solomon Dalung yace harbin motar Professor Ango Abdullahi da sojoji suka yi a garin Bauchi bai zama sabon abu ba.
Yace sun dade suna jin labarin cewa akwai shugabanin arewa da aka lissafa, wadanda aka ce sojoji da jami'an tsaro zasu halaka su.
Barrister Dalung yayi wannan furuci ne a hira da sashen Hausa yayi dashi akan budewa motar Professor Ango Abdullahi wuta da sojoji suka yi
Yace su a wurinsu wani yunkuri ne da gwamnatin Nigeria take yi na kashe shugabanin arewa. A saboda haka harin da aka kaiwa motar Professor Ango Abdullahi bai zama abun mamaki ba.
Barrister Dalung yace sun godewa Allah cewa Proifessor Ango Abdullahi da sauran mutanen dake cikin motar babu wanda yaji rauni. Yayi kira ga gwamnati data yi taka tsan tsan. Suma jami'an tsaro yace suyi taka tsan tsan.
Yace wannan hari abun kunya ne, kuma dattijan arewa zasu binciki al'amarin