A ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zaben da yake karatowa na Najeriya a ranar 28 ga watan Maris din 2015 da muke ciki, an koyar da wasu masu yi wa kasa hidima guda dubu 34 domin guduanar da aikin zabe.
Shugaban hukumar yiwa kasa hidima Janar Johnson Olawumi ya tabbatar wa wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin da haka. Ya kara da cewa, wadanda aka horar din tsofaffin dalibai ne da wa’adin hidimar kasarsu a yanzu ya kare ba tare da an yi zaben ba.
Don haka ya ce za su yi aiki kai tsaye ne a karkashin kulawar hukumar zabe. Wasu masu hidimar kasar sun nuna cewa ba wata matsala don an ce su yi aikin zaben tun da yana daga cikin rantsuwar da suka yi akan za su yi wa kasarsu aiki a matsayinsu na ‘yan hidimar kasa.
Amma wasu sun nuna fargabarsu kasancewar ana kaisu garuruwan da ba nasu ba ne, wasu ma ba su iya magana da harshen ‘yan garin da aka kaisu ba. Sun kuma nuna fargaba kan yadda a wasu lokuta ake ta da rikici a lokutan zabe ya ke kuma shafarsu.
Kaftin Hassan Mohammed mai ritaya, tsohon soja ne kuma ya taba aiki da hukumar ta masu yiwa kasa hidima, Ya kara hasken cewa idan aka yi la’akkari da abin da ya faru a zaben shekaru hudu da suka wuce ya kamata a kula sosai da yadda za a tura su aikin.