Kakakin jam'iyyar ta APC, Alhaji Lai Muhammad, ya ce jam'iyyarsa na da wani rahoto na musamman da suka samu cewa gwamnatin PDP na shirin yin amfani da hukumar EFCC ta kame shugabanninta.
Wadanda jam'iyyar ta yi zargin za'a kama din sun hada da Alhaji Asiwaju Bola Tinubu da kuma duk wasu jigajigan jam'iyyar masu fada a ji, musamman wadanda ke taimakawa jam'iyyar.
Alhaji Garba Wazirin Hausawan Sabo Yaba, wanda jigo ne shi ma a jam'iyyar ta PDP, ya ce abin da ke faruwa shi ne mutanen PDP sun rasa makama domin akwai lokacin da suka fada cewa Janar Buhari ya kamu da ciwo.
Ya kara da cewa batun kama shugabannin 'yan adawa ba zai yi tasiri ba domin idan sun yi hakan ba su kama talakawan dake goyon bayansu ba.
Ya Sabo Yaba ya kara da cewa abin da ake ciki yanzu shi ne babu wani dake sha'awar PDP.
To sai dai PDP ta musanta zargin inda ta ce babu kanshin gaskiya a zargin.
Mataimakin kakakin yakin neman zaben Jonathan Isa Tafida Mafindi ya ce ita hukumar EFCC ta na da dokokinta da majalisun tarayya suka gindiya mata.
A cikin dokokin ba'a fada masu wata jam'iyya za ta gaya masu lokacin da za su kama wani ba.
Ya ce zargin APC magana ce ta batawa mutane suna da kuma shafawa PDP kashin kaza da kuma neman kawo husuma a lokacin da aka kusa shiga zabe.
A cewarsa 'yan adawa su fadi duk abun da za su fada domin ranar 28 ga wannan watan 'yan Najeriya za su zabi Jonathan ya zama shugaban kasa.
Ya ce idan APC tana da mutanen dake da matsala da EFCC su je su kare maganarsu amma kada su sa sunan PDP ciki.
PDP inji Mafindi ba ta da hurumin ta fadawa EFCC ta kama wani ko ta saki wani.
Ga rahoton Babangida Jibrin.