Ba za a yi hanzarin fadin sakamakon zabukan 'yan majalisar dattawa ba a wasu muhimman jihohin Amurka a yau Laraba, yayin da wadanda ke rike da kujerunsu ke samun nasara a wasu jihohin. Jami’an zabe a fadin kasar sun yi gargadin cewa za a dauki kwanaki kafin a tabbatar da sakamakon wasu zabukan.
Gaba daya dai, yadda aka yi tunani ‘yan jam’iyyar Republican za su samu nasara ga dukkan alamu ba haka zancen yake ba, yayin da jam’iyyar adawar ke samun nasara a majalisar wakilai a wuraren da ba a yi tunani ba, duk da cewa jam'iyyar za ta iya samun isassun kujeru da za su sa ta samu rinjaye a majalisar.
A yanzu dai majalisar dattawan ta rabu daidai tsakanin ‘yan Democrat da ‘yan Republican, inda mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris za ta iya jefa kuri’ar raba gardama idan aka yi kunnen doki wajen zartar da kuduri, a yanzu dai ‘yan Republican na bukatar kujera daya kacal domin samun rinjaye a majalisar.