A yau Talata Amurkawa sun dunguma zuwa rumfunan zabe domin kada kuri’unsu a zaben sabbin ‘yan majalisar dokoki, zaben da ake ganin har ila yau zai yanke hukunci kan irin kamin ludayin shugabancin Donald Trump, lamarin da ya raba kawunan masu kada kuri’un.
Kujerun majalisar wakilai 435 ake takararsu, sannan ana takara akan kujeru 35 cikin 100 na majalisar Dattawa, baya ga haka akwai kujerun Gwamnoni 36 cikin jihohi 50 da su ma ake takara akansu.
Kwararru a fannin tattara ra’ayoyoin jama’a sun ce akwai alamu da ke nuna cewa jam’iyyar Democrat ta karbe rinjayen majalisar wakilai.
‘Yan jam’iyyar ta Democrat na bukatar lashe kujeru 23 ne kacal kafin su karbe ikon majalisar ta wakilai.
Su dai ‘yan jam’iyyar ta Republic, sun dogara ne da yekuwar shugaba Trump ta neman goyon baya, a kokarin da suke yi na ci gaba da rike rinjayen majalisar dattawa da suke da shi na kujeru 51 yayin da ‘yan Democrat ke da 49
Daga cikin kujerun majalisar ta dattawa 35 da za a yi takarar su, ‘yan Democrat na da 26 yayin da ‘yan Republican ke da tara.
Facebook Forum