Bayan nasarar da gwamnan jihar Taraba, Akitet Darius Dickson Isiyaku ya yi na wa’adi na biyu a zaben gwamnan jihar, ya bude sabon babi a Najeriya na cewa jam’iyyar PDP za ta shafe fiye da shekaru 20 tana mulkin jihar.
Gwamna Darius ya ce yana godiya da mutanan jihar Taraba yadda su ka fito kwansu da kwarkwatansu suka sake zabensa a wa’adi na biyu kuma ya ce zai nunka irin ayyukan da ya yi a baya.
A martanin dan takarar gwamna na jam’iyyar adawa ta APC kuma tsohon mukaddashin gwamnan jihar, Sanata Sani Abubakar Danladi, y ace za su kalubalanci wannan sakamakon zaben a gaban kuliya saboda ba'a yi zabe a wasu gurare da dama ba kuma ya yi zargin cewa tuni aka soma cin zarafin ‘yan adawa.
To sai dai kuma a nata martanin, tsohuwar Ministan Harkokin Mata kuma yar takarar gwamna a jam’iyyar UDP, Sanata Aisha Jummai Alhasan, tace ta rungumi kaddara, amma tana kira da gwamnan jihar Darius da ya rungumi kowa a gwamnatinsa.
Wannan dai na zuwa a daidai lokacin da hankula su ka fara kwantawa a jihar biyo bayan murnar sakamakon zaben.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul-aziz:
Your browser doesn’t support HTML5