A babban birnin tarayyar Abuja masu sa idon na cikin gida karkashin jagorancin cibiyar raya demokradiyya ta "Centre for Democracy and Development" da suke lura da yadda zaben ya gudana a sassa daban daban na Najeriya, sunce wannan karo zaben na gwamnoni da 'yan majalisun dokoki na jihohi a Najeriya yayi fama da wasu matsaloli iri iri.
An fuskanci matsaloli daga na'urar tantance masu kada kuri'a, yayin da a wasu wuraren ma baki daya aka ki yin amfani da na'urorin ba kuma tare da bayar da kwararan dalilai ba.
Rahoton masu sa idon da Farfesa Adelaja Jinadu da Uwargida Hidatat Hassan suka sanyawa hanu, ya nuna an sami arangama tsakanin wasu wakilan jam'iyyu da jami'an hukumar zaben Najeriya a mazabun Achida da Wurno a jihar Sokoto, yayinda a jihar Oyo akai ta uzurawa masu zabe al'amarin da ya razana da dama daga cikin masu kada kuri'a suka ki fitowa zaben.
Jami'an masu sa idon suka ce matsalar saye da saida kuri'ar wani babban koma baya ne da ya mamaye zaben na jiya inda akai ta cin kasuwar a fili karara, al'amarin da yasa hukumar EFCC ta cafke wasu fitattun 'yan siyasa a jihohin Benue da Kwara.
A jihar Kano ma masu sa idon sunga inda akai ta sayen kuri'a akan farashin da ya kama daga Naira dubu uku zuwa Naira dubu hudu.
A jihar Legas kuwa, masu sa idon sunce sunga ana tattara sunayen wadanda suka kada kuri'a da aka tsara rarraba masu Naira dubu daya da dari biyar biyar, sannan anyi amfani da kananan jam'iyyu wajen sayawa manyan jam'iyyu kuri'a.
Daga bisani masu sa idon sun nuna gamsuwa da yadda jami'an hukumar zaben suka isa tasoshin zabe akan lokaci ba kamar yadda aka fuskanta ba a yayin zaben shugaban kasa da akai makonni biyu da suka gabata.
Saurari cikakken rohoton Hassan Maina Kaina daga Abuja.
Facebook Forum