Rassan hukumar zaben Najeriya ta INEC a jihohin Pilato, Adamawa, Sokoto da Bauchi, sun bayyana cewa zabukan wadannan jihohi ba su kammalu ba.
A jihar Pilato, jami’in da ke tattara kuri’u a jihar, Farfesa Richard Anande, ya ce ya ayyana zaben ne a matsayin wanda bai kammalu ba, saboda yawan kuri’un da aka soke sun fi na ratar da aka samu tsakanin jam’iyya mai mulki ta APC da abokiyar hamayyarta ta PDP.
APC ta ba PDP ratar kuri’u 44,929, wadanda ba su kai yawan kuri’un da aka soke ba, wadanda yawansu ya kai 49,377.
A jihar Adamawa haka lamarin yake, inda adadin yawan kuri’un da jam’iyyar PDP ta bai wa APC na 32,476 ya haura adadin wadanda aka soke, wato kuri’u 40,988.
A can jihar Sokoto ma, hukumar zabe ta INEC reshen jihar, ya ayyana zaben jihar a matsayin wanda bai kammalu ba, domin adadin kuri’un da suka samar da rata, wato 3,413, tsakanin PDP da APC ya gaza kuri’u 75,000 da aka soke
A Bauchi ma, jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Muhammed Kyari, ya ba da umurnin soke zaben karamar hukumar Tafawa Balewa saboda adadin ratar ya sabawa kuri’un da aka soke.