Wannan na zuwa ne yayin da jami’an tsaro suka cafke wani hadimin gwamnan jihar da makamai da kuma katunan zabe 340.
Sakamakon zaman dar-dar a Jalingo fadar jihar Taraban, yanzu haka gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwar gaggawa, dake dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamnan jihar Hassan Mijinyawa, na kafa dokar hana fita a cikin Jalingo tun daga karfe shida na maraice har zuwa shida na safe.
Koda yake sanarwar bata bayyana dalilan kafa dokar hana fitan ba, amma gwamnatin ta bukaci jama’a da su zama masu bin doka da oda.
Kafin wannan sanarwar ma dai sai da aka samu hatsaniya a anguwar dake kusa da ofishin hukumar zabe inda ake bayyana sakamako.
Yayin da wannan ke faruwa jami’an tsaron farin kaya na DSS, sun kai samame gidan wani hadimin gwamnan jihar Taraban, inda suka samu makamai da kuma katunan zabe 340.
Nuhu Umar jami’in hukumar ta DSS ya tabbatar da lamarin, yayinda wani jami'in hukumar zaben ya tabbatar da katunan da aka kaman da cewa na hukumar zabe ne.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto an kawo sakamakon kananan hukumomi kusan goma, wanda jam'iyyar adawa ta PDP ke da rinjaye.
Ga rahoton Ibrahim Abdul’Aziz daga Jalingo.
Facebook Forum