Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Olukayode Egbetokun, ya bada umarnin takaita zirga-zirga a jihar Edo gabanin zaben gwamnan da ake shirin gudanarwa a gobe Asabar, 21 ga watan Satumbar da muke ciki.
Babban sufeton ‘yan sandan yace an yi haka ne domin tabbatar da cewa an dauki matakan da suka dace wajen gudanar da sahihin zabe cikin gaskiya da lumana.
A sanarwar da ya fitar yau Juma’a, kakakin rundunar ‘yan sandan, Muyiwa Adejobi yace babban sufeton ya ba da umarnin takaita zirga-zirgar ababen hawa akan tituna da hanyoyin ruwa da dukkanin nau’ukan harkokin sufuri tun daga karfe 6 na safe har zuwa 6 na yamma a ranar zaben.
Ya kuma kara da cewa wadanda umarnin ya tsame sun hada da, kafafen yada labaran da aka tantance da jami’an zabe da motocin daukar marasa lafiya da kuma ma’aikatan bada agajin gaggawa.
Akalla jam’iyyun siyasa 18 ne zasu fafata a zaben, inda manyan jam’iyyun suka kasance APC da PDP da kuma jam’iyyar Labour.