Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Samun Karin Bukatun Neman Yin Kiranye Ga ‘Yan majalisun Tarayya Da Na Jihohi - INEC


Hedkwatar Hukumar Zaben Najeriya INEC, Maitama Abuja
Hedkwatar Hukumar Zaben Najeriya INEC, Maitama Abuja

Mista Sam Olumekun, Kwamishina na kasa kuma Shugaban Kwamitin Bayar da Bayani da Ilimin Zabe na INEC, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis bayan taron shugabannin hukumar.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce ta samu bukatu da dama daga kungiyoyi daban-daban a fadin kasar, suna neman su yi wa wakilansu kiranye a majalisun tarayya da na jihohi.

Dokar zaben Najeriya ta ba masu zabe damar janye wakilansu a majalisu idan har suka kai wani adadi.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta fitar da sabbin Dokoki da Ka'idoji da aka gyara don janye 'yan majalisun tarayya da na jihohi, har da kansiloli a Majalisar Kananan Hukumomin Babban Birnin Tarayya (FCT).

Mista Sam Olumekun, Kwamishina na kasa kuma Shugaban Kwamitin Bayar da Bayani da Ilimin Zabe na INEC, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis bayan taron shugabannin hukumar.

Ya ce an yanke wannan shawarar ne tare da sake duba shirin karshe don zaben gwamna na jihar Edo wanda zai gudana ranar Asabar mai zuwa.

“Masu zabe a mazaba ne ke fara aiwatar da wannan tsari (kiranye). Hukumar tana aiwatar da bukatarsu daidai da Sassan 69, 110, da 160 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (da aka yi wa gyara) da kuma Sassan 2(c) da 113 na Dokar Zaɓe ta 2022."

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG