Hukumar zabe ta kasa INEC a Najeriya ta ce yakin neman zabe ya kare daga karfe 12 na daren Alhamis yayın da aka tunkari zaben Gwamna a jihar Edo
A ranar Asabar 21 ga watan Satumba za a yi zabe a jihar wacce ke kudu maso kudancin Najeriya.
"Hukumar na son tunatar da jam'iyyun siyasa cewa, Sashe na 94(1) na Dokar Zabe ta 2022, da kuma abin da ke kunshe a abu na 12 na Jadawalin Ayyuka don zaɓen Gwamnan Jihar Edo na shekarar 2024, dukkan kamfen na jam'iyyun siyasa za su kare da tsakar daren yau, (Alhamis) 19 ga Satumba 2024." Kwamishina na kasa kuma Shugaban Kwamitin Bayar da Bayani da Ilimin Zabe na INEC ya ce cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya kara da cewa, "saboda haka, an haramtawa wata jam'iyyar siyasa a jihar Edo ta gudanar da gangami, jerin gwano ko kamfen ta kafafen watsa labarai daga tsakar daren yau (Alhamis) kamar yadda doka ta sashe na 96 na Dokar Zabe ta 2022 ta ce.
Olumekun ya kara da cewa, a ranar zabe, Asabar 21 ga Satumba 2024, an haramtawa jam'iyyun siyasa, ‘yan takara da magoya bayansu zuwa rumfunan zaɓe da tufafin kamfen ko su ɗauki duk wani abu da ke nuna alamar jam'iyya.
Masu lura da al'amura na cewa, zaben zai iya zama zakaran gwajin dafi ga farin jinin gwamnatin APC mai mulki a matakin tarayya.
Dandalin Mu Tattauna