Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Bukaci A Gudanar Da Zaben Gwamnan Jihar Edo Cikin Lumana


Shugaban Najeriya, Bola Tinubu (Hoto: Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu (Hoto: Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Shugaban kasar ya roki ‘yan takarar gwamnan da jam’iyun siyasa da magoya bayansu dasu mutunta tsarin dimokiradiya da kuma zabin mutane.

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya bukaci dukkanin masu ruwa da tsaki a zaben gwamnan jihar Edo mai zuwa dasu gudanar da ayyukansu cikin lumana da mutunta juna.

An tsara gudanar da zaben ne a gobe Asabar, 21 ga watan Satumbar da muke ciki.

Sanarwar da mashawarcin shugaban kasa na musamman akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Juma’a, tace shugaban kasar ya roki ‘yan takarar gwamnan da jam’iyun siyasa da magoya bayansu dasu mutunta tsarin dimokiradiya da kuma zabin mutane.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa tsarin dimokiradiya na bunkasa ne a kan wayewa da juriya da hakuri da kuma mutunta ka’idojinsa.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar dasu kasance cikin lumana da mutunta juna a yayin zaben.

Haka kuma, Tinubu ya umarcesu dasu warware kowace irin takaddama ta hanyar lumana ta hannun hukumomin da doka ta amince dasu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG