Yankin Mubi na cikin wuraren da aka kwato cikin kwanakin nan. Al'ummar yankin sun ce ba za'a barsu a baya ba.
Mutane sai murna suke yi. Babu maganar Boko Haram. Jama'a na ganin sun warke daga ciwon da yake damunsu.
Su ma al'ummar Taraba sun bi sawun sauran kasar da fatan sabuwar gwamnatin zata sharewa al'umma hawaye. Sun yi fatan Janar Buhari ya kama mulki lafiya ya kuma gudanar da gaskiya ba tare da nuna bangaranci ba ko banbancin addini.
Matasa sun bayyana matsalolin da suke fuskanta kama daga rashin wuta zuwa rashin hanyoyi. Sun yi fatan gwamnatin Buhari zata kula dasu. Matasa suna son a yi masu adalci. Suna son zaman lafiya tare da aikin yi. Yakamata gwamnati ta kuma mayarda hankali akan makarantu, kiwon lafiya da makamantansu.
Wasu na ganin Najeriya a kulle take. Dole gwamnatin Buhari ta budeta domin ta samu yin walwala. Cin hanci, rashin doka, rashin tsaro da rashin sanin yakamata sun yiwa kasar katutu. Gwamnatin Jonathan ta mayar da kasar tamkar kasar da bata da doka ko gwamnati.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5