Rahotanni daga Najeriya na cewa shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya kira abokin hamayyarsa Janar Muhammadu Buhari inda ya taya shi murnar lashe zabe.
Wakilin Muryar Amurka da ke Abuja ya ruwaito cewa Mr Jonathan ya kira Buhari ne yayin da ya rage a bayyana sakamakon jiha guda, wato jihar Sokoto.
Tun a ranar lahadi aka fara kidayan kuri'un bayan kammala zaben na shugaban kasa da 'yan majalisu wanda aka fara a ranar 28 ga watan Maris.
Zaben na Najeriya ya kasance cike da rudani kama daga lokacin da ake yakin neman zabe ya zuwa lokaicn da aka gudanar da shi.
Da farko dai zaben zai gudana ne a ranar 14 ga watan Fabrairu amma aka dage bayan da jami'an tsaron Najeriya suka ce babu isassan tsaron da za gudanar da zaben.
Shi dai Janar Muhammad Buhari ya yi takara ne a karkashin jam'iyar APC yayin da shi kuma shugaba Goodluck Jonathan ya yi takara a karkashin Jam'iyar PDP.
Ita dai jam'iyar ta PDP ita ta yi ta tafiyar da ragamar mulkin kasar tun bayan da Najeriyar ta koma turbar dimokardiya a shekarar 1999.
Masu lura da al'amura sun ce wannan shi ne karon farko da jam'iya mai mulki ta taba fuskantar babban kalubale daga jam'iayar adawa.
Ku saurari karin bayani a hirar wakilinmu na musamman Ibrahim Alfah Ibrahim da Yusuf Harande.