Daya cikin jami'an sa ido na kasa da kasa akan yadda aka gudanar da zaben ranar Asabar Muhammad Danda wanda ya taba zama firayim ministar kasar Nijar yace akwai wasu matsaloli da yakamata a kawar.
Yace hukumar zabe ta jaraba sabbin kayan aiki wadanda ba'a bata yin anfani dasu ba a wurare da dama balantana ma a kasashen Afirka ta Yamma. Katunan zabe na din-din-din da naurar tantance masu zabe su ne abubuwa biyu sabbi da hukumar ta jaraba. Yace dole ne duk abun da ya zama ana jarabashi ne a samu matsala dashi. Saboda haka wani wuri naurar ta ki tashi, wato bata yi aiki ba. Wani wurin kuma da ta tashi zafi ya tilasta mata ta tsaya. A wani wurin kuma an yi jinkirin kawota
Duk wadannan matsalolin suka sa aka samu cikas a wasu wurare aka dauki lokaci kafin a fara zabe.Muhammad Danda yace suna fata wannan zai zama abun koyi ga hukumar domin su gyara saboda zaben gaba.
A Afirka ta Yamma ita ce kasa da tafi kowace yawan jama'a da yawana arziki. Saboda haka yin anfani da wasu sabbin kayan gudanar da zabe ka iya zama alheri ga nahiyar. Fatarsu ne Najeriya ta cigaba ta gyara kurakuren.
Sabbin kayan aikin da Najeriya tayi anfani dasu idan aka yi gyara suna iya taimakawa wurin kawar da koke-koken zabe a nahiyar Afirka domin zasu magance magudin zabe.
Daga karshe tarayyar Turai tayi alkawarin yin tur da duk wani yunkurin yin magudi a sakamakon zaben.
Ga rahoton Medina Dauda.