Zaben dai ya cika da sarkakiya idan aka yi la'akari da yadda aka jinkirta zaben da wasu kalamun tada hankali da zaman dardar da 'yan Najeriya suka shiga ciki.
To amma matakin da shugaban kasa mai barin gado Goodluck Ebele Jonathan ya dauka na mika fatar alheri tare da amincewa da sakamakon zaben ya gama tarihi a siyasar ta Najeriya.
Al'ummar yamma maso kudancin Najeriya inda mataimakin shugaban kasa na Janar Buhari ya fito su ma ba'a barsu a baya ba wajen bayyana farin cikinsu da wannan nasara.
Tun jiya ne aka fara wasannin ababen hawa a biranen Legas da kewaye domin nuna farin cikinsu da wannan nasara.
Alhaji Muhammad Bello wani shugaban al'umma ne a birnin Legas wanda ya yaba da yadda aka gudanar da zaben. Yace abun da ba'a yi tsammani zai faru ba ya faru domin ba'a san shugaba mai ci yanzu zai yi muba'aya dangane da sakamakon zaben ba tare da ja ba.
Wani mazaunin layin Ikorodu ya bayyana nashi ra'ayin. Yace abun da ya bashi mamaki shi ne shi bai taba ganin irin wannan bikin ba a Najeriya.
Alhaji Inuwa Yahaya na jam'yyar APC cewa ya yi nasarar daga Allah take.
Ga rahoton Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5