Hukumomi a Jihar Rivers sun saka dokar hana fita bayan da aka yi wata zanga zanga yayin da aka bayyana sakamakon zaben jihar.
A daren jiya gwamnatin jihar ta ba da umurnin kowa ya zauna a gida bayan barkewra rikici.
Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Ahmad Muhammad ya ce gwamnatin ta yi hakan ne saboda ta kare rayuka da dukiyoyi.
“Ita gwamnatin jiha ta duba ta ga ya cancanta a saka wannan doka saboda a kare duk wani abu da zai biyo baya na tashin hankali.” In ji Muhammad.
Game da batun lokacin da za a dage dokar, kakakin y ace za a duba a tabbatar cewa al’amura sun daidata kafin a dage dokar.
“Ita dai gwamnatin jiha ta ce za ta duba taga har sai al’amura sun daidaita sannan ta fara sassautawa har zuwa lokacin da ta ga ya dace a janye dokar.” Ya kara da cewa.
Rundunar ‘yan sadan ta kuma musanta zargin da ke cewa an harba yaji mai saka kwalla akan masu zanga zangar.