Jami'in yace a zaben shugaban kasa Janar Muhammad Buhari na jam'iyyar APC ne ya lashe zaben shugaban kasa da kuri'u dubu dari uku da saba'in da hudu da dari bakwai da daya yayinda shugaban kasa Jonathan ya tashi da kuri'u dubu dari biyu da hamsin da daya da dari shida da sittin da hudu.
Barrister A.P.Shehu kwamishanan shari'a na jihar Adamawa da ya wakilci jam'iyyar PDP a wurin bada sakamakon zaben yace halin rayuwa ke nan. Yau kai ne amma gobe ba kai ba ne. Yace dole yadda rayuwa ta zo a karbeta haka. Yace babu abun da zai hanasu amsa sakamakon zaben tunda sun sa hannu a kai.
Daraktan kemfen din Janar Buhari na jihar Adamawa Alhaji Ibrahim Hassan ya nuna farin cikinsa da sakamakon. Yace sun ji dadi da nasarar kuma Allah ya tabbatar masu da nasara a kasar gaba daya.
A sakamakon zaben 'yan majalisa tsohuwar shugabar APC a jihar Binta Garba Mafi ta lashe kujerar majalisar dattawa na mazabar Adamawa ta arewa. Ta doke gwamnan jihar Bala John Ngilari na PDP.
A jihar Taraba ma an soma samun sakamakon zaben 'yan majalisar dattawa da na wakilai.Dan takarar jam'iyyar PDP Marafa Bashir Abba ya lashe zaben. Ya bayyana farin cikinsa da yiwa Allah godiya da jama'a da suka goyi bayansa..
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.