A zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya an samu matsalar rashin kai kaya kan lokaci zuwa fumfunan zabe. Haka ma naurar tantance masu zabe ta kasa aiki a wasu wurare.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar a jihar Filato yace domin tabbatar da ba'a samu tsaiko wajen raba kayan zaben ba shi ya sa suka yi hakan tun ranar Talata musamman a wurare masu nisa da hedkwatarsu. Babbar matsalar da suka samu a zaben da ya gabata ita ce rashin kwarewar wasu ma'aikatan da hukumar ta dauka aiki na wucin gadi. Wasu a cikinsu basu iya yin anfani da kayan aiki ba duk da horon da hukumar ta basu.
Jami'in yace ya zama dole su sallami wasu ma'aikatan da basu iya aiki ba suka mayarda gurbinsu da wadanda suka tabbatar zasu iya aikin yadda ya kamata.
Ya ja kunnuwan wasu 'yan siyasa dake cewa hukumar na canza ma'aikatanta ne da nufin tafka magudin zabe. Ya sake cewa rashin iya aikinsu ne ya sa suka canzasu.
Su ma 'yan siyasa sun ce sun shirya domin lashe zaben. Jam'iyyar PDP tace ta shirya tsaf domin shirinsu na yanzu ya fi na farko. Wani kuma mai magana da yawun APC yace zasu fito su kawo canji a Filato kamar yadda suka kawo canji a gwamnatin tarayya.
Ga rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5