Da zarar mutum yaje zabe, kuma katin sa ne wanda hukumar zabe ta bashi. Na'urar tantance kati zata baiyana suna da dukkan bayanan da aka dauka a lokacinda mutum yayi rajista.
Nick Dazan, mukadashin direktan hulda da jama'a na hukumar zaben Nigeria shi yayi wannan bayani a hira da Sahabo Imam Aliyu yayi dashi.
Mr. Dazan yace duk wanda yaje da katin jabu domin yin zabe, to yayi aikin banza, domin katin ba zai nuna dukkan bayana da aka dauka ba, kamar addreshi da lambar waya da sauran bayanin da mutum ya bayar a lokacinda aka yi masa rajista.
Yace za'a yi tantancewar ne a gaban yan jarida da masu lura da zabe da wakilan jam'iyun siyasa da kuma dukkan wadanda ya kamata, a saboda ayi adalci.
A saboda haka masu saye da sayar da katuna zaben su, sunyi aikin banza domin a gare su kwaliya ba zata biya kudin sabulu ba.
Your browser doesn’t support HTML5