Jama'ar Gombin sun tuntubi hukumar zabe ta INEC inda suka mika kokensu to amma an fada masu wai sai an je Abuja tukunna.
Wani Alhaji Rahama yace rashin katunan zaben ya sasu cikin zullumi. Garin Gombin yana cikin garuruwan da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram a jihar Adamawa. Jama'ar wurin na cigaba da kokawa da rashin samun katunan zabensu na din-din-din wato PVC.
A wata sabuwa kuma rahotanni daga wasu sassan jihar na cewa wasu shugabannin kananan hukumomi da kansiloli sun yi awangaba da katunan zabe masu dimbin yawa da nufin rabawa magoya bayan 'yan jam'iyyar da suke so..
Alummar kananan hukumomin Michika da Madagali sun bayyana cewa an fada masu su je santa amma da suka je sai aka fada masu shugabannin kananan hukumominsu da kansiloli sun amshe katunan. Wata ta ce an karbe masu katunansu ne da sunan za'a yi masu wani abu amma har yanzu shiru kamar an shuka dusa.
Sabon kwamishanan hukumar zabe na jihar Adamawa Alhaji Abba Yususf yace hukumarsa tana binciken badakalar kuma duk wanda aka samu da hannu ciki za'a hukuntashi.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.