A wata hira da Muryar Amurka, Kakakin hukumar zabe (INEC) Mr. Nick Dazan ya fadi cewa duk masu aikata wadannan abubuwan sun san kansu, amma har yanzu babu wanda ya bada wata hujja ko makasudin zanga-zangar da neman cire shugaban hukumar zaben.
Tarihin Najeriya ya nuna cewa yawancin Shugabannan hukumar zabe na fuskantar kalubale musamman bayan sun gama aikinsu.
Mr. Dazan ya fadi cewa Farfesa Jega ya lashi takobin yiwa ‘yan Najeriya adalci, ya kara da cewa da mamaki ace wasu na so yayi murabus, don tun lokacin daya yi rantsuwar gudanar da aikin shi bai baude ba.
Ya zuwa yanzu dai ya rage ‘yan kwanaki kadan a kai ga babban zabe, amma wasu na nuna rashin amincewar su akan yin amfani da na’urar nan ta tantance katin zabe. Wasu ma na rade-radin cewa za a kawo wani kwararre da zai yi wata dabara da zata hana na’urar aiki. Amma Mr. Dazan yace babu abinda zai hana yin amfani da wannan na’urar.
Game da batun raba katin zabe kuma, Mr. Dazan yace ya zuwa yanzu sun raba kusan kashi tamanin da biyu cikin dari da katunan Kuma ana cigaba da buga sauran da suka rage, ana kuma ta rabawa.