Taron majalisar ministoci na yammacin ranar Alhamis 6 ga watan Yuli ya sanar cewa kashi 25.2 % na dalibai suka yi nasara a jarabawar Baccaluareat da aka rubuta a fadin Nijer a karshen watan yunin da ya gabata.
Jarabawar na da nufin tantance wadanda suka cancanci samun takardar shaidar kammala makarantun share fagen shiga jami’a.
Hakan ya nuna cewa an sami koma bayan da girmansa ya haura kashi 3 cikin dari idan aka kwatanta da jarabawar da aka yi a shekarar 2022, yayin da aka dora alhakin faruwar kan kura-kuran da ke tattare da abubuwan da aka bukaci daliban rukunin D su rubuta a fannin lissafi wato Matematiques.
Mafari kenan da ya sa shugaba Mohamed Bazoum ya ba da umurni a bai wa daliban da abin ya shafa damar sake gwada sa’arsu, a cewar wata sanarwa.
Masana sha’anin karatun boko sun yaba da daukar wannan matakin, ko da yake har yanzu akwai sauran gyara.
Da yake bayyana matsayinsa akan wannan mataki sakataren kungiyar SYNAFCES ta malaman sakandare Jariri Labo ya yaba da shi domin a cewarsa, yin haka shi ne adalci ga dalibai da iyayensu.
Shi ma shugaban kungiyar Voix des Voix Alhaji Nassirou Saidou na da irin wannan ra’ayi, koda yake ya yi jan hankali akan bukatar daukar matakan don kada a sake tafka kuskuren da aka aikata a baya.
Dalibai 92,956 ne suka rubuta jarabawar Baccalaureat a bana. Sai dai tarin matsalolin da aka ci karo da su ya sa kungiyoyin malamai da na kare hakki a fannin ilimi suka yi ta kiraye-kirayen ganin hukumomi sun dauki mataki ciki kuwa har da maganar sake duba tafiyar hukumar tsara jarabawar Baccalaureat wace ake ganin son rai ya yi kaka gida a sha’aninta, hasalima komai na tsare tsare na gudana ba tare da hannun malaman sakandare ba.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5