Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zulum Ya Shammaci Wasu Malaman Firaimare Da Jarabawar Ba-zata


Gwamna Zulum a zaune a aji yana yi wa malamai jarabawa (Facebook/Gwamnatin Borno)
Gwamna Zulum a zaune a aji yana yi wa malamai jarabawa (Facebook/Gwamnatin Borno)

A cewar gwamna Zulum, ba an gudanar da jarabawar ba ne don a kori wani malami a aiki, sai dai don a auna kwarewarsu don a san inda za a saka su.

Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi wa wasu malaman makarantar firaimare da ke garin Baga jarabawar ba-zata.

Zulum ya yi wa malaman jarabawar ne don a gwada cancantarsu a fannin koyarwa a cewar wata sanarwa da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na sada zumunta.

Gwamna na ziyarar aiki ne a garin na Baga wanda ya yi fice a harkar sana’ar su a yankin Tafkin Chad, inda har ya kwana daya a garin

Gwamna Zulum a tsaye (Facebook/ Gwamnatin Borno)
Gwamna Zulum a tsaye (Facebook/ Gwamnatin Borno)


“Zulum ya fadawa malaman cewa, ba an gudanar da jarabawar ba ne don a kori wani malami a aiki, sai dai don a auna kwarewarsu don a san inda za a saka su.” Sanarwar ta ce.

A cewar Zulum, wadanda ba su da kwarewa a fannin koyarwar, za a ba su zabin a mayar da su wata ma’aikata ko kuma a tura su su karo ilimi.

Zulum ya ce a karshen kowacce shekara, za a rika auna ilimin kowanne malami da dalibi, sannan gwamnati za ta tallafa masu da wurin zama da sauran ababen more rayuwa.”

Malamai suna jarabawa a garin Baga (Facebook/Gwamnatin Borno)
Malamai suna jarabawa a garin Baga (Facebook/Gwamnatin Borno)

Sanarwar ta kara da cewa, bayan da aka kammala jarawabar, gwamna Zulum ya sanar da ba da tallafin naira dubu 20 da yadin shadda goma-goma ga kowanne malami.

“Muddin idan har za ku ba da gudunmowar da za ta tallafawa al’uma, za mu tallafa maku, za kuma mu rika yi maku jarabawa, sannan wadanda ya kamata a kara masu albashinsu za a kara masu.” In ji Zulum.

XS
SM
MD
LG