Daliban Najeriya dake gudun hijira tare da iyayensu a jihar Diffa sun fara jarawabar kawo karshen karantun Sakandare a cikin jihar ta Diffa,
Diffa, Nijar —
A shekarun baya dai daliban na Najeriya na zuwa ne kasarsu domin gudanar da wannan jarabawar. A Bana, dalibai 160 ‘yan Tarayyar Najeriya dake zaman gudun hijiar a jihar Diffa tare da iyayensu tun cikin shekarar 2014 ne ke gudanar da wannan jarabawar ta kawo karshen karatun sakandare,
Ganin cewa, a bara daliban ba su samu damar gudanar da jarabawar ba saboda karancin tallafi ya sa Gwamnatin Nijar da ta Najeriya suka dauki wani mataki na bai daya domin daliban na Najeriya su samu gudanar da wannan jarabawar a jihar ta Diffa inda suka zaman gudun hijra.
Ministan ilimin Jamhuriyyar Nijar Frofesa Ibrahim Na Tatou shine ya jagorancin bikin soma wannan jarabawar.
A nasa bangaren jakadan Tarayyar Najeriya dake zama a Nijar, Malam Djalo Sani ya yaba matuka game da yadda hukumomin kasashen biyu suka shirya wannan jarabawar.
Suma dai daliban Najeriya dake gudanar da wannan jarabawar sun nuna farin cikinsu game da yadda aka tsara wannan jarabawar a jihar ta Diffa,
Ganin irin shekarun da ‘yan gudun hijirar na Najeriya suka kwashe a jihar ta Diffa,a yanzu haka masu fashin baki kan sha’anin ilimi a jihar ta Diffa, sun fara bayar da shawara ga hukumomin ilimin Nijar, na ganin sun bude wani sashe na musamnman da zai kula da bayar da ilimin Turanci a jami’ar Diffa domin wadannan daliban su samu damar ci gaba da gudanar da karantun a jihar ta Diffa.