Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Yaki Da Cin Hanci Ta Aika Jami'anta Don Zuba Ido A Jarabawar Dalibai


HALCIA - Nijar
HALCIA - Nijar

A jamhuriyar Nijar, hukumar yaki da cin hanci ta sanar cewa ta aika da jami’anta zuwa sassan kasar da nufin dakile dukkan wata cuwa cuwa a jarabawar da daliban ajin karshen makarantun sakandare a matakin farko za su fara rubutawa a gobe Talata 13 ga watan Yunin 2023.

Gwamnatin Nijar da kanta ce ta ba hukumar izinin shiga tsare tsaren dukkan jarabawar da za a yi a kasar don ganin an kawo karshen korafe korafen iyayen daliban game da satar jarabawa.

Sauyin da aka samu a shekaru biyun da suka gabata sakamakon shigar da hukumar yaki da cin hanci a jerin jarabawar da aka gudanar a Nijar ya sa mahukuntan kasar bai wa hukumar ta HALCIA izinin saka ido a illahirin jarabawar da za a yi a nan gaba; dalilin da ya sa kenan hukumar ta aike da jami’anta zuwa cibiyoyin jarabawar Brevet wato ta ajin karshen makarantun sakandare a matakin farko da ake farawa a wannan Talata 13 ga watan Yunin 2023 a fadin kasar.

Kungiyoyin cigaban jama’a irinsu Voix des sans Voix, a ta bakin shugabanta Alhaji Nassirou Saidou, na ganin matakin a matsayin wata hanyar bai wa kowane dalibi damar samun sa’ar da ke daidai da ta dukkan sauran takwarorinsa.

A baya hukumar yaki da cin hanci ta kama dalibai da malamai har da wasu shugabannin cibiyoyin jarabawa saboda samunsu da yunkurin sata. Lamari na baya shi ne wanda ya wakana a yayin jarabawar daliban sakandare ta 2022 saboda haka ta gargadi masu ruwa da tsaki su nisanci kansu da aikata dukkan wani abin da ke kama da rashin gaskiya.

Lura da yadda a baya cin jarabawar makaranta ko ta neman aikin gwamnati ta fara yi wa dan talakka wuya saboda yadda cuwa cuwa ta fara samun gindin zama ya sa mahukuntan Nijar shigo da tsarin tura jami’an hukumar yaki da cin hanci zuwa cibiyoyin jarabawa, nasarorin da aka samu a samakaon wannan mataki ya sa gwamnatin bai wa hukumar ‘yancin shiga al’amuran tsare tsare a illahirin jarabawar da za a yi a wannan kasa don ganin an faro abin tun daga tushe.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG