Sun bukaci da a gurfanar da tsohon shugaban kasar ne tare da wasu mutane su goma sha uku bisa laifukan da suka hada da kisa da azabtarwa, da cin zarafi, tare da tilatsa bacewar bakin hauren da adadinsu ya kai 67 duk ya’yan Afrika ta Yamma.
Sai dai ba wannan kadai bane, hukumar ta TRRC ta bukaci gwamnatin Gambia ta samarwa al’ummar da wannan al'amarin ya shafa, diyyan 612,000 na dalolin Amurka, a cewar wani mista Martin Kyere, daya daga cikin bakin hauren da suka kubuta daga hannun dakarun tsohon shugaban Gambiyan.
A ranar 22 ga watan Yulin 2005 ne dakarun tsaron Gambiya suka cafke bakin haure da aka ce su duka ya’yan Afrika ta Yamma ne bisa zarginsu da yunkurin kifar da gwamnatin Yahya Jammeh a daidai lokacin da kwalekwale mai inji da ke dauke dasu ya tsaya a Gambiya, suna kan hanyar tsallake tekun meditereniya zuwa nahiyar Turai.
A cikin kwana 10 aka kashe bakin hauren da suka hada da ‘yan Ghana 44, da ‘yan Nigeria guda 9, da ‘yan Togo su 2 tare da wasu mutanen Cote Divoire da Senegal da kuma wani ‘dan Gambiya, dab da iyakar Senegal da Gambiya sannan aka saka gawarwakinsu acikin wata rijiya.
Yayin wani taro da manema labaru a birnin Kumasi a jihar Ashantin kasar Ghana Mista William Nyarko shugaban kungiyar JUSTICE2JAMMEH da ta tsaya tsayin daka domin kwato hakkin al’ummar da akaci zarafinsu ya jinjinawa kwamitin tare da bukatar da gwamnatin Adama Barrow na Gambiya da ta sake duban kudin diyyan saboda yayi kadan.
Sai dai kuma hukumar TRRC ta bukaci a kafa kwamitin binciken kasa da kasa domin gano hakikanin wurinda gawarwakin suke don afito dasu..
Saurari rahoto cikin sauti daga Hamza Adam:
Your browser doesn’t support HTML5