Bincike ya nuna cewa, yara mata masu shekaru 15 zuwa 19 basua zuwa makaranta alokacin da suke al'ada bisa dalilin rashin kudin sayan audugar amfani.
Wannan lamarin ya ja hankalin Ameenata Koita mai fafutukan kare hakkokin bil Adama, wadda tayi tattaki daga Amurka zuwa Ghana tare da tallafawa yara mata dalibai da kofin al'ada wanda mata zasu iya anfani da shi har na wa’adin shekara goma batare da ya lalace ba, inda dalibai 450 suka ci moriyar kyautar.
Ameenatu ta ce zata ci gaba da neman karin taimako domin fadada rarraba kofin a Ghana tare da kasashe masu fama da talauci a Nahiyar Afrika.
A karshe ta yi kira ga kungiyoyin kare hakkokin bil Adama ciki har da Majalisan Dinkin Duniya da su maida hankali sosai bisa wannan al’amari saboda hakki ne akan kowa da ya bada nasa gudunmuwa domin ganin duniya ta samu kyakyawan makoma.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hamza Adam: