‘Ya’yan Makiyaya a Nigeria

‘Ya’yan Makiyaya a Nigeria

‘Ya’yan makiyaya dake karatu zasu dara nan bada jimawa ba, domin hukumomin ilmi a Nigeria na daukan matakan bunkasa fannin ilmin ‘ya’yan makiyayan.

A rahoton da wakilin Sashen Hausa na muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz ya aiko na dauke da bayanin cewa ana bunkasa yin karatu a ruga domin kwadaitawa ‘ya ‘yan Fulani makiyaya zama suyi karatu. Sama da shekaru goma ke nan da kaddamar da shirin bunkasa fannin ilmin makiyaya a Nigeria amma shirin har yanzu na samun cikas.

A jihar Adama wakilin sashen hausa na Muryar Amurka ya nemi jin ta bakin daya daga cikin shugabannin irin wadannan makarantu na ilmin ‘ya’yan makiyaya Malam Jibril Abdulrahman wanda yayi bayanin irin matakan da hukumomi ke dauka domin bunkasa shirin. Yace matsalar da ake fuskanta it ace gano hanyar da za’a bi a kwadaitawa ‘ya’yan makiyaya muhimmancin ilmi maimakon bin shanunsu daga nan zuwa can. Yace tunda so ake yi a basu ilmin ba sun eke son yin karatun ba, lallai sai an tashi haikan wajen kwadaita masu muhimmancin ilmi.

Shima babban jami’in hukumar bunkasa ilmin bai daya a jihar Adamawa Dr. Salihu Bakari Girie yayi Karin haske kan matakan da humarsa ke dauka domin bunkasa fannin ilmin ‘ya’yan makiyaya a jihar Adamawa baki daya.

Aika Sharhinka