Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Farashin Tikitin Jirgin Sama Ya Janyo Cin Tara


British Airways (file photo)
British Airways (file photo)

Hukumomin Nigeria sun ci tarar kamfanin jiragen sama Ingila na “British Airways” da “Virgin Atlantic” kudi masu yawan gaske saboda Karin farashin tikitin jirgin saman da suka yiwa fasinja ba bisa ka’ida ba.

Jami’an hukumar kula da zirga-zirga da filayen jiragen sama a Nigeria yau Alhamis suka bada sanarwar cin tarar kamfanin British Airways kudi Dala miliyan $135, shi kuma kamfanin jiragen saman Virgin Atlantic aka ci tararsa kudi Dala miliyan $100. Jami’an na Nigeria sun yi zargin cewa kamfanin jiragen saman biyu sun hada kai a shekarar 2004 suka rika kara kudin tikitinsu babu kakkautawa wanada hakan ke cutar da aljihun fasinja a Nigeria. Jami’an na Nigeria suka ce an kai ga cin tarar kamfanonin biyu ne bayan wani binciken da aka gudanar na tsahon watanni shida. Kamfanonin biyu British Airways da Virgin Atlantic sun musanta cewar suna cutar da aljihun fasinjan dake shiga jiragensu.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG