Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ke daurewa Boko Haram gindi


Jami'an tsaro suna yin sintiri a jihar Borno dake arewa-maso-gabashin Nigeria.
Jami'an tsaro suna yin sintiri a jihar Borno dake arewa-maso-gabashin Nigeria.

Hukumomi a Nigeria sunce wasu masu “hannu da shuni” ne ke daurewa kungiyar Boko Haram gindi.

Hukumar leken assirai ta Nigeria tace wasu hamshakan ‘yan siyasa attajirai ne ke samarwa kungiyar Boko Haram kudaden da take anfani da su wajen gudanarda hare-haren da take kaiwa a Nigeria. A ranar Litinin din nan ne Hukumar SSS take fadar cewa kamun da tayi wa wani mai magana ne da yawun Boko Haram, ya nuna cewa wannan kungiyar tana samun tallafi da daurin gindi daga wasu hamshakan ‘yan siyasa masu fada- a ji. Hukumar SSS tace wanda ta kama din, mai suna Ali Sandi Umar Konduga yana yi wa wani babban dan siyasa na jihar Borno ne aiki, don shine yake aika sakkoni da sunan kungiyar ta Boko Haram, inda yake anfani da lakabin “Usman al-Zawahiri.” Hukumomin Nigeria dai sun jima suna zargin Boko Haram da kai hare-hare da dama, wadanda kuma aka sha asaran rayukka barkattai a cikinsu. Galibin hare-haren duk kana kaisu ne a jihar Borno koda yake kuma Boko Haram ta dauki alhakkin farmakin da aka kai kan opishin Majalisar Dinkin Duniya dake Abuja inda har mutane 23 suka hallaka.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG