Wadanda Harin da Aka Kai a Jihar Adamawa ya Rutsa Dasu Suna Cikin Mawuyacin Hali-Inji Shugabannin Yankin

Daya daga cikin wadanda suka sami rauni a harin da aka kai a kauyen Waga Chakawa a jihar Adamawa.

Shugabannin yankin Madagali Suna yunkurin kai wadanda harin da 'yan bindiga suka kai a yankin zuwa babban asibiti dake Yola.
Mutane da suka sami raunuka sakamkon harin da 'yan bindiga suka kai a kauyen Waga Chakawa a karamar hukumar Madagali cikin jihar Adamawa, suna cikin wani mawuyacin hali, yayinda shugabannin suke kokarin ganin an kawarda wadanda suke da munanan raunuka zuwa babban asibiti dake Yola babban birnin jihar.

Da yake magana da wakilin Sashen Hausa, daya daga cikin shugabannin karamar hukumar Maina Ularamu yace raunukan da wadansu suka samu suna da tsanani. Baya ga jinyarsu, karamar hukumar tana kokarin samar da kayan abinci da sauran wasu bukatu ga mazauna kauyen sakamakon wannan hari da aka kai musu.

Kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, wanda shine yake wakiltan yankin a majalisar dokokin jihar, ya kai ziyara yankin inda ya ya bada gudumawar kayan abinci, yayinda hukumomi suke laluben hanyoyin magance matsalolin tsaro da 'yan bindigan suke kara haddasawa a yankin.

Ga Karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Harin Waga Chakawa