Wadannan mutane maza da mata, sun fito ne daga jihar Jigawa, kuma sun isa can a cikin wasu motocin bas-bas.
Hukumomin 'yan sanda sun tsare su bisa zargin ko su na da alaka da kungiyar Boko Haram, amma shugabannin al'ummar arewacin Najeriya a Fatakwal sun ce wannan zargin ba ya da tushe.
Wata mace daga cikin wadanda aka tsare ta fadawa wakilin Muryar Amurka, Lamido Abubakar Sokoto, ta wayar tarho cewa an binciki duk kayansu, da motocinsu da kuma jikinsu, amma babu wani abu da aka samu wanda yayi kama ko ya alakanta su da wani abinda ba na halal ba.
Haka kuma, an dauki hotunan yatsunsu, amma har yanzu ba a sake su ba.
Kwamishinan 'yan sanda a Jihar Rivers, ya tabbatar da tsare mutanen, amma ya ki yarda yayi karin haske kan dalilin da yasa har yanzu ake ci gaba da tsare su.
Shugabannin al'ummar Arewacin Najeriya a Fatakwal sun tafi ofishin 'yan sandan inda suka ce ba zasu ja ba har sai sun tabbatar da an bi kadin wannan lamarin.