Daya daga cikin shugabannin karamar Mina Ularamau ta tabbatarwa wakilin sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz aukuwar lamarin. Yace 'Yansanda da suka kai doki sun fada kofar rago da 'yan bindigan suka yi musu suka kashe wani jami'in 'Yansanda mai mukamin ASP da kuma kofur daya. Haka kuma sun lalata motar da 'Yansandan baki daya.
A cikin bayanin da wani mazaunin kauyen wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya yiwa wakilin Sashen Hausa, yace da farko maharan sun kai hari ne kan wani coci inda suka jefa bam, daga bisani suka shiga gidajen wasu farar hula suka kama su suka tafi dasu. 'Yan uwansu da suka bi sawu sun gano gawarwakinsu a mafitar kauyen.
Shugabanni da mazauna kauyen duka sun ce maganin wannan al'amari shine a girke jami'an tsaro a yankunan domin sa ido kan irin wadan nan hare hare.