Neja na Sauraron Jama'a Kan Kundin Tsarin Mulki

  • Ibrahim Garba

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan

Jihar Naija ta bi sahun jihar Kano wajen shirin sauraron ra'ayoyin jama'a kan shirin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Yau Talata Majalisar Dokokin jihar Naija za ta gudanar da taron sauraron ra’ayoyin mutanen jihar game da niyyar sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar.

Wakilinmu na jihar Naija Mustapha Nasiru Batsari ya ce daga cikin abubuwan da za a tattauna akai har da batun kananan hukumomi - musamman maganar bas u ‘yancin cin gashin kai.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Naija Hon Adamu Usman ya shawarci mutanen jihar da su hallara sosai wurin taron saboda ra’ayoyinsu su yi tsasiri saboda duk abin da jama’a ke so shi ne su ma za su amince da shi.

Shi kuwa Shugaban marasa rinjaye a Majalisar Dokokin ta jihar Naija Hon Nuruddin Umar ya ce tuni ma su ka fara karbar ra’ayoyin mutane game da kananan hukumomi. Ya ba da misalin cewa ana korafin cewa ba za a iya biyan albashin malaman makaranta ba, saboda har yanzu ana biyan tsohon bashi. Don haka ya ce idan aka mayar da batun biyan malaman makaranta ga kananan hukumomi yaya za su biya?

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dokoki 1