Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP ta Tafka Asara a Jihar Taraba


PDP
PDP

Wasu 'yan jam'iyyar PDP a jihar Taraba sun ce sun binne jam'iyyar kuma sun koma SDP sabili da dauki dora da suke zargin uwar jam'iyyar tayi masu.

'Yan jam'iyyar sun ce ba zasu yi jam'iyyar ba kuma domin babu adalci. Wai dan takarar da aka kawo masu basu sanshi ba.

Sun lissafa manya manyan 'yan jam'iyyar da suka fice daga PDP suka koma SDP. Sun nuna fushinsu ne akan abun da suka kira sauki dora da jam'iyyar tayi masu a can Abuja a zaben fidda gwanin kujerar gwamnan.

Ita dai uwar jam'iyyar ta baiwa Darius Ishaku kujerar dan takarar gwamnan jihar Taraba din ne. Batun ya jawo cecekuce inda ma har sabuwar jam'iyyar SDP ta shirya karbar kusoshin jam'iyyar PDP tare da basu takara. Amma kuma wasu wakilai 400 suna shirin kai PDP kotu domin wai ba'a barsu sun kada kuri'a ba.

Wakilan sun ce ba'a yi zabe ba sabili da haka zasu garzaya kotu. Idan har shugabannin jam'iyyar basu duba lamarin da idon harama ba to ko shakka babu zasu yi watsi da jam'iyyar.

To saidai yayin da wasu ke kokawa wasu ko murna su keyi. Marafa Bashir Abba wanda PDP ta baiwa kujerar dan takarar majalisar dattawa a Taraba ta tsakiya yayi murna tare da godiya ga Allah.

Ga rahoton Ibrahim Abdul aziz.

PDP ta Tafka Asara a Jihar Taraba - 3'14"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG