Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Dage Raba Katin Zabe Na Din-din-din a Jihar Neja


Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega.
Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Attahiru Jega.

Dama hukumar ta sa ranar yau Jauma'a a matsayin ranar da zata fara raba katin zaben.

Yanzu hukumar tace ta sake sa ranar 19 zuwa 22 na wannan watan da zata fara raba katin zabe na din-din-din a duk fadin jihar. Madaki Muhammad Wasi kakakin hukumar zaben mai kula da jihar Neja ya bayyana dalilin sake ranar.

Babban dalilin da ya sa hukumar ta dage ranar zaba katin shi ne rashin gama katunan cikin lokacin da hukumar tayi zato. To amma sake dage lokacin bai yiwa al'ummar jihar dadi ba.

Rabaran Musa Dada shugaban kungiyar kiristoci ta CAN a jihar yace dage ranar bai yi ba domin lokaci ne da kiristoci suke shirin bikin sallar kirsimati. Yawancin mutane basa yin kirsimati a wuraren da suke zama. Sukan yi tafiya a lokacin da hukumar tace zata fara raba katin.

Ita ma kungiyar Izala mai wa'azin addinin musulunci tace lamarin nada ayar tambaya. Malam Sanusi Erana wanda yayi magana da yawun kungiyar yace suna ganin kamar wata makarkashiya ce ake yi domin a hana wasu 'yancinsu.

Malam Muhammad Awal shugaban kungiyar guragu yace abun takaici ne. Dage-dagen na iya haifar da wasu manufofi iri-iri. A ganinsu wani salo ne na cin kudin gwamnati.

Duk da korafe-korafen hukumar zaben tace jama'a su kwantar da hankalinsu kamar yadda kakain hukumar ke cewa. Ya bukaci jama'a su hakura komi zai kankama.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG