ALIYU MUSTAPHAN SOKOTO: anzu dai Allah Ya sa Jam’iyyar APC ta tsayar da kai takarar shugabancin kasa, daga nan wani mataki zaka dauka na gaba bayan barin Legas?
MUHAMMADU BUHARI: To yanzu abu na biyu shine, batun abokin takara.
ALIYU MUSTAPHAN SOKOTO: To a ina ake game da wannan abokin tafiya?
MUHAMMADU BUHARI: To har yanzu dai bamu fito waje ba, mun fadi ko wane ne, kuma ko daga ina, muna so sai munga yadda kuri’ar take, tunda an samu dubu uku, da maitan da arba’in. Muna so mu san daga ina aka fi samun kuri’un, ko kuwa daga ina zamu fi samun kuri’u idan aka kai ga zabe na badi. Domin babban abunda zai tasiri shine a ci zaben.
ALIYU MUSTAPHAN SOKOTO: Kafin a zo ayi wannan zaben, munyi ta jin sunaye da maganganu iri-iri ana magana tikitin Musulmi da Musulmi, ko Musulmi da Kirista, Yarabawa ko Igbo da sauransu. A kalla ma iya sanin hasashe na kowani yanki abun zai fito, koda ba’a yi maganar addini ko kabila ba?
JANAR MUHAMMADU BUHARI: A’a, bazan so in fadi ba a yanzu a gaskiya, saboda wato abubuwa na siyasa sunyi karfi yanzu, batun sha’anin addini. Har ma ta kai sai da nayi wa wasu magana, nace su lura, shekara tara Janaral Gowon yayi da yawancin manyan hafsoshin soja masu mulkin sojan kasa, dana ruwa, dana sama, da kuma mataimakinshi a fadarshi duk Kirista ne, babu wanda ya taba magana. Sannan da abiola yazo, aka fara siyasa, ya dauki Kingibe daga Borno, Musulmi da Musulmi. Kuma an tabbata da gwamnati lokacin tayi adalci, ta su suka ci zabe. Duk ‘yan Najeriya sun san wannan. Sannan kuma da aka zo aka sake, canzawa muka koma soja, da ni da marigayi Tunde Idiagbon Allah Ya gafarta mishi duk Musulmi ne mu, kuma daga arewa, babu wanda ya taba yin magana. To saboda haka, wannan sabon izgilin nan, wato na batun sha’anin addini an kawo shi amma kuma izgilin yana da karfi kwarai da gaske, saboda haka yanzu wanda za’a dauka sai anyi shawara da jam’iyya, an kuma yi shawara da mutane, wadanda muka san suna da nisan hankali, sannan a fadi ko wanene zai zama abokin takara din.
Janaral Muhammadu Buhari shine dan takarar jam’iyyar APC mai adawa a Najeriya, bayan samun nasara akan ragowar ‘yan takara 4 a zaben fidda gwani wanda aka kamala a birnin Ikko dake kudu maso yammacin Najeriya. Janar Buhari zai kara da shugaba mai ci yanzu, Goodluck Jonathan.