Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Yace Za'a yi Kacha-Kacha da PDP


Buhari da Jonathan.
Buhari da Jonathan.

Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tattauna da Janar Muhammadu Buhari, tsohon shugaban kasa kuma dan takarar jam'iyyar APC mai adawa game da nasarar da yayi, da kuma batutuwan da jama'a yanzu suke muradin sani. Aliyu Mustaphan Sokoto yayi hira da Janar Buhari.

Aliyu Mustapha: Wace rawa abokan takara sauran guda hudu nan zasu taka wajen tabbatar da nasaran zaben da za’a yi badi?

Muhammadu Buhari: A yau dai guda uku sunyi alkawari, da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Turaki Adamawa, da Rabiu Musa Kwankwaso, da Rochas Okorocha, sunyi Magana, a yau sun ce su kamar yanda jamiya, tasa akayi yarjejeniya, cewa idan aka ci zabe za’a goyi bayan duk wanda ya ci domin a karfafa jamiya, domin a ciye zabe mai zuwa na badi, amma Sam Nda Isiah, bai halarci wurin ba.

Aliyu Mustahpa: Shin kayi mamakin yawan kuri’un da ka samu dubu uku da wani abu ?

Muhammadu Buhari: A gaskiya ban yiba saboda wadan da suke cikin Najeriya, yanzu suke kuma yin siyasa sun san cewa ‘yan Najeriya, yawancinsu yanzu sun harzika duk imda kaje mutane cewa suke sun gaji, wato rashin tsaro din nan, na daya na biyu lalacewar arzikin kasa, ma’adunai, an rufesu, matasa da yawancin ma’aikata basu da aikin yi, zai zaman kasha wando, sai sace-sace sai kisan kai sais ace mutane, a anshi kudin fansa, wato kasar dai ana cikin mugun tashin hankali, saboda haka duk inda kaje a kasar, gabas da yamma, kudu da arewa kukan dasu keyi kennen,saboda haka inda aka samu aka yi zaben kan ka’ida, Gwanatocin PDP bama na tarayya kadai ba za’a yi masu kacha-kacha a badi inda Allah ya yarda. Saboda mutane sun gaji da lalacewar arzikin kasa.

Aliyu Mustapha: Ranka ya dadai kasan kafin a zo ayi zaben nan mun sha maganan nan da kai mutane na cewa ka san PDP suma sun san kai, ku sha karawa mai zai banbanta a wannan karon da za kuyi a 2015?

Muhammadu Buhari: Abun da ni keso ya banbanta shine abun da mutanen Oshun sukayi, ni nayi Imani PDP, ba zata dena zalunci ba, saboda haka aabun da za’ayi shine fadakarwa ga dukkan mazabu, jama’a, su tabbatar da cewa kuri’arsu sunyi tasiri, wannan kadai ne magani abun, mun gani a Ekiti, mugani a Oshun, a Ekiti, akwai alamar anyi sakaci amma a Oshun, da aka tashi tsaye babu irin harbe-harben da ba’ayi ba cikin iska, an kuma kama mutane abokan hamayya amma mutane suka dage dole aka hakura aka barwa Ra’uf, Gwamnatin shi ‘yan Najeriya sun san da haka saboda idan suna son a canja Gwamnati, sai sun tashi tsaye kuri’unsu, sunyi tasiri, idan kuma suka ki yin zabe suka yi kwaciyarsu wannan fitina, na rashin tsaro a kasa gaba daya zata zama hantsi leka gidan kowa.

Aliyu Mustapha : Mutane PDP, sun saba cewa mun san Buhari Mun saba kada Buhari menene-menene ko da gaske su keyi ko kuma ta maza ce sukeyi suna cewa abamu Buhari, domin mun san shi gashi Allah ya sake kawo masu Janar Buhari, kuma kai ka san su a can baya kayi ta korafe-korafe gamaida yanda ake harkar magudin da sauransu Me zai banbanta wajen daura damarar da APC, zata yi a zabe, mai zuwa da zai hanna suyi abunda akayi can baya?

Muhammadu Buhari: Abun da zai banbanta shine abunda na fada daman a fadi kila ake sato wasa nakeyi sa da abun ya kasance, shine mutane su tabbata kuri’arsu tayi tasiri, alalmisali da mukayi wannan sabuwar jamiyar, wato aka hade akayi All Progressive Congress, APC, a kowace mazaba akalla muyi rajistan mutane dari-dari, cikin mutane dari-dari akowace mazaba baza ka rasa mutane goma wadanda ‘yan jamiyar ne masu biyeyya, saboda haka ba zasu yarda a hada kai da suba ayi magudi, daga nan har zuwa unguwani har zuwa karamar hukuma har kuma zuwa jiha, Saboda haka za muyi tsari sosai yanda mutane zasu kare kuri’unsu, suyi tasiri, kamar yanda gwamnatin Oshun tayi ya zamana ita ke da Gwamnati inda aka kada na Ekiti.

Aliyu Mustapha: A karshe mai ka keso ka gayawa ‘yan Najeriya, dangane da wannan nasaran dakuma abun da zasu sa ran su gani mai kuma ka ke harsashe zai faru a jihohi, dagane da zabe mai zuwa da kuma jamiyar ka ta APC?

Muhammadu Buhari:To a gaskiya abun da na saba fadi ne kamar shekaru ashirin da biyar da suka wuce, duk dan Najeriya, baida wata kasa sai Najeriyan, nan saboda haka gwamma kowa ya zage damtse, mu tabbatar da wannan tsari na demokradiya, shi yafi alheri, idan ana zabubbuka masu tasiri, amma idan aka bari ana sace kuri’u, ko kuma ana wani magudi da ban ana cancansawa a tafi gidan Radiyo, a fadi sakamaon zaben da ba ayiba, ko aka yi akayi banza da shi, ace mutun ya tafi wurin sharia, wanda ke nemen abinci gobe inna yaga kudin da zai baiwa, manya-manyan lauyoyi, abunda dan karan rikici har zuwa kotun koli, iyaka dai sai yace Allah ya isa, wannan taron Allah ya isan wata kila shine ma ya tsiyata kasar, na zalunci da aka diga yiwa masu karamin karfi saboda haka dama munyi Magana akan cewa jiki magayi,to wannan ya tabbata ba haka aka so ba.

Buhari Yace Za'a yi Kacha-Kacha da PDP - 7'08"
please wait

No media source currently available

0:00 0:08:17 0:00

Kasar Kamaru ta sha fama da matsalar yaduwar bayanan karya a game da zabuka a baya, lamarin da ya janyo rudani a shafukan sada zumunta
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:04:23 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Kudurin wasu 'yan Najeriya na sabuwar shekara a fannin lafiya, da wasu sauye-sauyen da suke fatan yi don samun nasara a rayuwarsu
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p

No media source currently available

0:00 0:05:16 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 1080p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG